Ad Code

Karamci ne ga Ƴan Jarida: Jinjina ga Shugabanci Majalisar Dokoki...

KARAMCI NE GA 'YAN JARIDA......
JINJINA GA SHUGABANCIN MAJALISAR DOKOKI KARO NA 8TH A KATSINA BISA  GA HAKAN.

Masu iya magana kan ce idan ba ka iya kyauta ba toh! Ka ba wanda ya ke ba ka,sannan duk dadin Sarewarka idan ba ka kirara kan ka da ita ba, wani zai are ta maka zambo .

A Dawowar Mulkin Dimokaradiya a Nijeriya musamman wannan Jamhuriyar da muke ciki, ta zo da samun damarmaki na samun mukamai dadama ga al'umma,inda a hannu daya Ma'aikatan gwamnati suma suke samun mukamai na wucin-gadi masu tsoka da tagomashi,musamman wadanda suka taka rawa cikin tafiyar siyasa ko kuma wasu suka taka a madadinsu.

Toh! Ko ma wace irin rawa aka yi DAN JARIDA rawarsa ta musamman ce a tafiyar Dimokaradiya. 

Amman kash ! Kash!!
A mafi akasarin tafiyar ana cin yaki sai abar DAN JARIDA da 'Kuturin Bawa' Ma'ana ko dai ya kasance aci kasuwar da waninsa da ya fi shi Uwa a Gindin Murhu ko kuma sai ya sake wani kamun Kafa da fadanci,idan yana son hakarsa ta cimma ruwa, sannan a Dama furar da aka nema tare da shi.
Amman a wannan karon a Jahar Katsina, Shugabancin Majalisar Dokoki a Karkashin jagorancin Alhaji Nasiru Yahaya Daura ya wankewa 'yan Jarida kurar da aka dade ana bada masu,bayan Mota ta ta shi.

Da farko bayan, Majalisar ta samu Shugabanci a dukkan matakai,wanda Allah ya zabi Alhaji Nasiru Yahaya Daura a matsayin jagora, la'akarin da ya fifita shi ne samarda Jami'ai na musamman da zasu jagoranci bangaren yada labaru na Majalisar( Media  Team) wanda ya kara fadadawa,saboda baiwa aikinsu muhimmanci.Inda a iya cewa ya bi tsari da aka so kowacce Majalisa ta  samar, saboda sanin muhimmancinsu a tafiyar da mulki a Dimokaradiyance  wato (Complete Vibrant Forth of the Relm Team)a turance.

Wannan babbar dama da Shugaban Majalisar ya samar ta sanya Jami'ai da dama irin Aminu Magaji Idrees, Suleiman Gambo
 K/Bai,Abdul Yusuf, Muntari Abba Usman suka samu mukamai dabam-dabam, duk a karkashin yada labaru na wannan Majalisa karo na 8TH 

Wani abin burgewa da ya cancanta a fadi duniya ta sani dukkan wadannan Jami'ai 'yan cikin gida ne,da ake dawainiyar yau da kullum da su a bangaren yada labaru,Shugaban ya dam damkawa Dokin tare da ragamar .

Bayarda wannan babbar dama da Majalisar ta yi,karamci ne da ake ganin ba a taba samun irin ba a matakai dabam-dabam,na irin wadannan wurare,koma an samu ba irin wannan ba.

Kazalika, Shugaban Majalisar Dokoki karo na takwas,Alhaji Nasir Yahaya Daura,ya bayarda mukaman nan batare da la'akari da siyasa ko sanayya ko tuntubar ra'ayin wani ba,face ya jinjina nauyin sune kawai ta hanyar sanin nagartarsu a aikace.

Irin wannan tagomashi mafi akasari koya samu sai an kai ruwa rana,in ma ta yiwu,amman ga Malam, Comrade,Honourable Nasiru Yahaya Daura shi Kiransu ya yi daidaikun su,tare da yi masu albishir na basu mukaman da kalaman karfafa guiwa. 

Kodayake dana shiga zuciyar Shugaban Majalisar nan,na gano yana da bukatu da muradun da yake son cimmawa  a Shugabancinsa,da ya kunshi yin aiki da wanda ke aikinsa,magance samun gibi a fagen yada labaru, sannan ya nuna cewar ko mutum bai san kowa ba,zai samu a dama da shi,in dai zai iya damawa yarda ya dace.

Ga wadannan Jami'ai, roko na gareku shi ne ku tabbatar da yakinin da ake da shi akanku. Tabbas! Kuma kwalliya zata biya kudin sabulu. Da yardar Allah 


   Mun gode!
Alkalamin Yakubu Lawal Dan Jarida 
Jami'in Hulda da Jama'a

Post a Comment

0 Comments